ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sinawa: Mutane Masu Kwazo Da Girmama Baki Da Ke Kallon Alkiblar Kawo Ci Gaba

by CGTN Hausa
3 years ago
Sinawa

A kwanan nan na karanta wata tattaunawa da aka yi da hamshakin attajirin nan na duniya, shugaban kamfanin Tesla and Space X, Mista Elon Musk da yake bayyana cewa, “Na shafe lokaci mai yawa a kasar Sin kuma na sadu da shugabanni a lokuta da dama… yadda yawancin mutanen kasar suka kasance masu kaifin basira, da aiki tukuru na da matukar ban mamaki.” in ji shi, kuma ya kara da cewa akwai mutane masu kaifin basira da dabara da aiki tukuru a kasar Sin fiye da na Amurka.

Wadannan kalaman nasa sun mayar da ni fagen waiwaye adon tafiya game da ziyarar da muka kai kasar Sin a ’yan shekarun baya.

  • Ya Kamata Kasashen Turai Su Kara Fahimtar Kasar Sin Don Karfafa Dangantakar Dake Tsakaninsu
  • An Fitar Da Rahoto Game Da Nazarin Yadda Ake Raya Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Fuskar Kare Hakkin Dan Adam

Tun daga filin jiragen sama na Shanghai da muka sauka na shaida yadda Sinawa ke da kwazon aiki. Kowa ka gani babu wasa a bakin aikinsa kama daga jami’an tantance fasinjojin da suka shigo kasa har zuwa otel da za ka yi masauki.

ADVERTISEMENT

Ziyarar da muka kai tashar teku mai zurfi ta Yangshan dake Shanghai ta sake bude min ido a kan kwazon Sinawa bisa yadda suka yi nisa wajen samar da ababen more rayuwa a kasarsu, musamman yadda suka gina gadar Donghai mai tagwayen titunan mota mai nisan kilomita 32.5 a saman teku. Sannan saman tudun da suka yi gine-gine a tashar ta Yangshan su ne suka samar da kusan kashi 90, tsibirin da suka cimma a wurin bai wuce kashi 10 ba.

Ko da yake, za mu iya cewa, gadar Donghai wasan yara ce idan aka kwatanta da gadar Danyang-Kunshan wacce ta sada wasu biranen lardin Jiangsu na kasar da a halin yanzu ita ce gada mafi tsayi a duk duniya, tana da nisan kilomita 164 (mil 104).

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Bugu da kari, yanzu haka, sabo da kwazon aiki da Sinawa ke da shi, kididdiga ta nuna sun gina titunan mota tsawon kilomita miliyan 5.35 a fadin kasar. Misalan kwazon Sinawa ta fuskar tattalin arziki na nan birjik, ko ba komai zamowar Sin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki ya isa shaida.

Da yake a zamanin nan, hankula sun karkata ga fannin bunkasa kimiyyar fasahar sadarwa, Sinawa ba a bar su a baya ba, limamai ne a wannan bangaren. Na gane wa idona abubuwa na ci gaban fasaha da kamfanin Huawei ke kerawa a lokacin da muka ziyarci reshensa na Shanghai. Kowace fasahar da aka samar walau aiki da jirgi mara matuki da fasahar 5G da birnin zamani wadda komai na’ura ke yi abubuwa ne na mamaki, amma babu wanda ya fi burge ni kamar wata fasahar kiwon shanu da Sin ta samar wadda manomi ke sanin halin da shanunsa ke ciki daga inda yake kwance ba tare da ya shigo cikin garke ba.

Sinawa na da kyakkyawan tsari a duk abin da suka sa a gaba kamar yadda muka gani a wuraren tarihin da muka ziyarta a Shanghai da Beijing irin su katafaren ginin Oriental Pearl Tower, babbar ganuwar Great Wall, fadar sarakuna ta Forbidden City, wurin bauta na Temple of Heaven da sauransu.

Ina da yakinin tsokacin da attajiri Elon Musk ya yi game da Sinawa a ’yan kwanakin nan za su tuna wa duk wanda ya taba ziyartar Sin da irin karamcin Sinawa da mamakin kwazonsu da ake koyar da su tun suna kanana kamar yadda na zama ganau ba jiyau ba.

Tabbas, tsare-tsare da kyakkyawar alakar da Sin ke ci gaba da kullawa da kasashen duniya don cin moriyar juna musamman mu a nan Afirka ta hanyar Dandalin Tattunawa na FOCAC, manuniya ce ga alkiblar da suka sa gaba ta kawo ci gaba ga duniya.

Sinawa
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

MASU ALAKA

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai
Daga Birnin Sin

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya
Daga Birnin Sin

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026
Daga Birnin Sin

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
Next Post
Sin: Ya Kamata Kwamitin Sulhu Ya Kara Daukar Matakai Kan Lokaci Don Inganta Tsagaita Bude Wuta Da Kawo Karshen Yaki A Dukkan Fannoni

Sin: Ya Kamata Kwamitin Sulhu Ya Kara Daukar Matakai Kan Lokaci Don Inganta Tsagaita Bude Wuta Da Kawo Karshen Yaki A Dukkan Fannoni

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.