Kasar Sin ta bayyana adawarta ga aniyar Amurka, ta sayarwa yankin Taiwan makamai, tana mai kira ga bangaren Amurka da ya janye wannan aniya nan take.
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ce ta bayyana hakan a Juma’ar nan, a matsayin martani ga amincewar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi, da batun sayarwa yankin Taiwan makamai na dala miliyan 300.
- Sin Na Fatan Amurka Na Yin Wani Abun A-zo-a-gani Na Tallafawa Farfadowar Nahiyar Afirka
- Zimbabwe Ta Yaba Da Jarin Da Kasar Sin Ta Zuba A Bangaren Makamashi Mai Tsafta Na Kasar
Da yake tsokaci kan lamarin, kakakin ma’aikatar tsaron Sin Zhang Xiaogang, ya ce Amurka ta keta alfarmar manufar kasar Sin daya tak a duniya, da yarjejeniyoyin hadin gwiwa 3 wadanda Sin da Amurka suka amince, musamman ma sanarwar ranar 17 ga watan Agusta, kuma hakan ya yi matukar keta hurumin ‘yancin kan kasar Sin, da tsaro da moriyarta. Kana hakan ya jefa tsaro, da daidaito a mashigin tekun Taiwan cikin halin rashin tabbas.
Zhang ya jaddada cewa, batun Taiwan jan-layi ne na farko da ba zai yiwu a tsallaka shi ba a dangantakar Sin da Amurka, Kuma ta hanyar ingiza aniyar ‘yan aware masu neman ’yancin kan Taiwan, sannu a hankali Amurka na hankada Taiwan cikin yanayi mai matukar hadari, wanda zai illata ita kanta Amurkan. (Saminu Alhassan)