A baya-bayan nan, gwamnatin kasar Mali ta sanar da cewa, an kai wasu hare-haren ta’addanci guda biyu a arewacin kasar, lamarin da ya haddasa hasarar rayukan fararen hula da dama. Daga bisani gwamnatin ta ayyana zaman makoki na kasa.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin tana jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su, da ma iyalan wadanda lamarin ya shafa da wadanda suka jikkata, tare da nuna adawa matuka ga duk wani nau’in ayyukan ta’addanci.(Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp