Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce kasar sa na matukar adawa da duk wata nau’in cudanya a hukumance, tsakanin mahukuntan yankin Taiwan da kasashen da suka kulla huldar diflomasiyya da Sin.
Wang ya bayyana hakan ne a Litinin din nan, yayin taron manema labarai da ya gudana, lokacin da yake tsokaci game da tambayar da aka yi masa, dangane da ziyarar da wasu ‘yan majalissar dokoki su 3 daga kasashen Estonia, da Lithuania da Latvia suka kai Taiwan.
Jami’in ya jaddada cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan yanki ne na kasar Sin da ba za a iya balle shi ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp