Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na adawa da matakin Amurka na fadada yankunan tudu na teku dake karkashin ikonta zuwa fadin da ya zarce nautical miles 200, matakin da a cewar jami’in na kara nuni ga ayyukan Amurka, na aiwatar da matakan kashin kai da danniya.
Wang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Talatar nan, ya jaddada cewa, matakin na kashin kai da Amurka ta dauka ya sabawa doka kuma haramtacce ne. Kaza lika hakan ya yi matukar sabawa dokokin kasa da kasa, ya gurgunta moriyar daukacin sassan kasa da kasa, kana ba zai samu amincer kasashen duniya ba.
Har ila yau, a cewar jami’in na Sin, matakin na Amurka karara ya bayyana yadda take tunkarar cudanya da sauran sassa, da halinta na nuna danniya, wanda ke shafar hatta dokokin kasa da kasa, ta yadda ta kan amince ko ta yi watsi da su gwargwadon bukatarta.
A cewar jaridar “Financial Times” ta Amurka, a baya-bayan nan kasar ta sanar da fadada ikonta na yankunan tudu na teku zuwa sama da nautical miles 200, matakin da ya mayar da karin sassan teku masu kunshe da albarkatun sinadarai karkashin ikon kasar.
Sakamakon hakan, tawagogin kasashen Rasha, da Sin, da wasu karin kasashe sun bayyana yayin taron kasa da kasa na hukumar lura da yankunan teku ta duniya cewa, Amurka ta ki rattaba hannu kan dokar kasa da kasa ta kare teku, wanda hakan ya ba ta damar fadada yankunan tudu na teku da take iko da su, kuma hakan ba abu ne da za a amince da shi ba. (Saminu Alhassan)