Kasar Sin ta bayyana matukar rashin gamsuwa tare da adawa da barazanar Amurka ta kakaba karin harajin kaso 10 kan kayayyakin kasar dake shiga Amurkar, bisa fakewa da batun maganin Fentanyl.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ne ya bayyana haka a yau, yayin taron manema labarai da aka saba yi a kullum, inda ya ce kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace na kare muradun da hakkokinta.
Lin Jian ya kara da cewa, kasar Sin ta sha nanata cewa, babu mai cin nasara daga yakin cinikayya da haraji, yana mai cewa, karin harajin da Amurka take yi ita kadai, ya take dokokin hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, haka yana illata muradun kasashen biyu da na duniya baki daya.
Haka zalika cikin wata sanarwa a yau, ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin ta ce, kasar na adawa da barazanar karin harajin kaso 10 da Amurka ke yi kan kayayyakin Sin bisa kafa hujja da batun Fentanyl. Sanarwar ta kara da cewa, idan Amurka ta nace kan bakanta, to, Sin za ta mayar da martani domin kare hakkoki da muradunta. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp