Ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin, ta bayyana a yau Litinin cewa, kasar na adawa matuka da matakin Amuka na tuhumar kamfanoninta a hukumace, dangane da batun kwayar Fentanyl.
A cewar ma’aikatar, wannan wani salon cin zali ne karara da Amurka ta dauka domin tattara abun da take kira da shaidu amma ba bisa ka’ida ba, ta hanyar gudanar da wani aikin yaudara, domin kaddamar da tuhume-tuhumen.
Ma’aikatar ta kara da cewa kasar Sin na da tsauraran manufofin yaki da miyagun kwayoyi, kuma ita ce kasa ta farko a duniya da ta sanya Fentanyl da ma abubuwan da suke da alaka ita cikin jerin miyagun kwayoyi, lamarin da ya taka muhimmiyar rawa wajen hana samarwa da safara da ma shan fentanyl, tana mai cewa, kasar Sin za ta kare halaltattun hakkoki da muradun kamfanoninta. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)