ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 3

by Nuhu Ubale Ibrahim
3 years ago
Layya

Layya da tumaki da awaki ta fi falala a Malikiyya, sannan shanu sai kuma raƙuma, amma tumaki sun fi awaki falala. Kuma maza na kowanne jinsin dabbobi da aka ambata ya fi mata falala. Duba; Alma’ūnatu Alã Mazhabi Ãlimil Madinati [1/485] da Arrisãlatu [shafi na 108] da Alkãfi [shafi na 238].

Ana yin layya ne da dabbar da take lafiyayyiya ƙosasshiya, ban da gurguwa da gurguntakarta ta bayyana a fili da mai ido ɗaya da rashin ganin idon ya bayyana a fili, ban da mara mai da ɓargo, ban da mara lafiya da rashin lafiyarta ta bayyana a fili. Duba; Muwaɗɗã Malik tare da Almuntaƙã Sharhul Muwaɗɗã [4/152-153] da Assamarud Dãnī [shafi na 392-393] da Aljawãhiruz Zakiyyati [shafi 144) da Alkãfi (shafi na 238) da Hashiyatud Dasūƙī ( 2/119] da Attaju Wal Iklil [4/336].

  • Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 4
  • Zan Iya Yi Wa Mamaci Layya?

Waɗannan sifofi guda huɗu ijma’i ne a Mazhabar Malikiyya cewa ba a yin layya da duk dabbar da ta sifanta da wata sifa daga cikin sifofin. Duba; Assamarud Dãnī [ shafi na 393].

ADVERTISEMENT

Babba don tana ɗingishi da ba za a iya kiranta gurguwa kaitsaye ba, haka mai gani gararagarara za a iya yin layya da ita. Duba Almuntaƙã
[4/152-153].

Fa’ida: Duk dabbar da take mahaukaciya ko mai ɗoyin baki ko mai ciki ƙwajaja to ba za a yi layya da ita ba domin tana cikin marasa lafiya. Duba Sirãjus Sãliki [2/9-10] da Amuntaƙã [4/153].

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

Akwai wasu abubuwa na aibi da aka ambata da suke hana a yi layya da dabbar da take da su, amma akwai saɓanin a kansu, shi yasa na kawar da kai daga ambatonsu, domin magana mafi inganci shi ne; basa hana a yi layya da dabbar da take ɗauke da su.

Mustahabbi ne ga wanda zai yi layya ya nisanci yanke ƙumba (farce) da yin askin gashin jikinsa daga ranar ɗaya gawatan Zul-hijja izuwa ranar sallah. Duba Muktasarul IKalil [shafi na 123] da sharhinsa Al-Ikhlilu [1/301] da Jawãhirul Iklil [1/221]

Wasu malaman suna ganin har wanda za a sanya shi a layya ba zai aske kowanne gashi na jikinsa ba ko farcensa. Duba Bulgatus Sãliki [1/287] da Hãshiyatus Sãwi Ala Assharhi Assagir da aka buka tare da Assharhu Assagir [2/341]

Mu haɗu a rubutu na 4

Nuhu Ubale Ibrahim
(ABU RAZINA PAKI)
10/12/1442
Bugu na biyu

Layya
Nuhu Ubale Ibrahim
+ postsBio
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 23
  • Nuhu Ubale Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/nuhu-ubale-ibrahim/
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 22

MASU ALAKA

Layya
Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
Layya
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
Bakon Marubuci

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

August 28, 2026
Next Post
Matawalle Bai Saci Kudin Jihar Zamfara Ba — Anas Kaura

Matawalle Bai Saci Kudin Jihar Zamfara Ba — Anas Kaura

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.