Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin, ya ce gwamnatin Sin na kira ga kasar Amurka, da ta dakatar da yunkurin ta na murkushe kamfanoni, da daidaikun jama’ar kasar Sin ba gaira ba dalili, karkashin takunkuman da take sanyawa kasar Iran.
Cikin wata sanarwa da kakakin ya fitar a shafin yanar gizo na ma’aikatar ta kasuwanci, game da sabbin takunkuman Amurka kan kasar Iran, ya ce Sin za ta dauki matakan da suka wajaba, don tabbatar da ta kare hakkoki, da moriyar kamfanoni, da daidaikun jama’ar ta bisa doka. (Saminu Alhassan)