Kwanan baya, Sin ta sanar da sabuwar manufarta ta kandagarkin COVID-19, inda ta fitar da sabbin matakan tuntubar jama’a tsakaninta da ketare, kasashe da dama na maraba da hakan.
Amma wasu kasashe sun dauki matakin kandagarkin wucin gadi kan fasinjoji daga kasar Sin. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labarai Talatar nan cewa, Sin na fatan kara tattaunawa da kasashen duniya don shawo kan cutar tare, kuma a ganinta, wasu matakan da aka dauka na kayyade Sinawa shiga kasashensu ba bisa gaskiya da matakai na kimiyya ba, abu ne da ba za a amince da su ba.
Ban da wannan kuma, a cewarta, Sin za ta mai da hankali matuka kan ba da tabbaci kan ziyarar da shugabannin kasar za su kai a ketare da sauran manyan ayyuka, don bayyana sabon yanayin bunkasuwar jam’iyyar JKS da sha’anin kasar bisa sabon takarfi a sabon zamani. (Amina Xu)