Manufofin kasar Sin na bude kofa ga kasashen waje na ci gaba da bude sabon babi na cika alkawarinta na bude katafariyar kasuwarta ga duniya domin cin moriyar juna da kuma tabbatar da gina al’umma mai makoma ta bai-daya ga bil’adama.
Matakan da kasar ke dauka na kara bai wa masu kamfanoni na duniya tabbaci da kwarin gwiwa game da alfanun zuba hannun jari a kasar, inda a karkashin hakan ne ma kasar ta kafa dokar kamfanoni masu zaman kansu wacce ta zo da sahihiyar hanyar bai wa kamfanonin kariya a kan moriyarsu.
- Me Ya Sa JKS Mai Tsawon Tarihin Sama Da Shekaru 100 Ta Dore A Kan Mulki
- Arsenal Ta Sayi Kepa Daga Chelsea
A ranar 20 ga watan Mayun shekarar 2025 ne aka fara aiki da dokar ta bunkasa tattalin arzikin bangare mai zaman kansa ta kasar Sin, wadda ta zama wata muhimmiyar doka ta farko da kasar ta kafa ga kamfanoni masu zaman kansu. Kasar Sin ta bullo da matakan da suka dace don kara samar da daidaito, da adalci, da gaskiya da kyakkyawan hasashen yanayin kasuwanci, tare da samar da damammaki masu yawa ga sashen na tattalin arzikin ’yan kasuwa masu zaman kansu.
Dokar ta nuna sakin mara da ba da tabbaci ga duk masu sha’awar zuwa kasar Sin don gudanar da harkokinsu na kasuwanci tare da karyata masu yamadidin cewa kasar Sin tana cin bulus, ma’ana ita za ta zo ta ci kasuwa a wata kasa fiye da kima amma kuma ta kankame nata.
Wasu jakadun kasashe a kasar Sin da suka zamo ganau ba jiyau ba sun yi tsokaci game da kyakkyawan tasiri da damammakin da dokar ta samar. Daga jawabansu, ana iya fahimtar dalilin da ya sa suka yi na’am da dokar da kuma abin da ya sa take janyo hankulan masu zuba jari na kasashen waje.
Jakadan Pakistan a kasar Sin, Khalil Rahman Hashimi ya ce, “sabuwar dokar ta bayar da karin kariya har ma da wani sauki na musamman ga kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin. Akwai tanade-tanade da dama a kasar Sin wadanda suke bayar da kwarin gwiwa ga kamfanoni masu zaman kansu don su iya bunkasa harkokinsu da kuma ba da gagarumar gudummawa ga tattalin arzikin kasar Sin. Akwai samun moriya da dama da kuma goyon bayan gwamnati har ma da ba da kariya ta fuskar shari’a ga kamfanoni masu zaman kansu.”
Shi ma jakadan Nepal a kasar Sin, Krishma Prasad Oli ya ce, “dokar ta sahale wa kamfanoni su gudanar da ayyukansu ba tare da wani matsi ba. Akwai babbar dama da aka samu a halin yanzu saboda akwai takamaimiyar doka da ta bayar da damar shigar kamfanonin kasashen ketare cikin hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin kuma suna iya yin aiki tare.”
Tuni dai aka fara ganin alherin sabuwar dokar bisa yadda ’yan kasashen waje ke tururuwar kafa kamfanoni da harkokinsu na kasuwanci a kasar ta Sin. Sakamakon amanna da kafuwar dokar da kuma fara aikinta, an kafa kamfanoni da ’yan kasuwa na kasashen waje suka zuba jarinsu fiye da 24,000 a cikin watanni biyar na bana kamar yadda ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta tabbatar a ’yan kwanakin nan. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp