A baya bayan nan, kasar Sin ta gabatar da bayani game da yanayin gudanar tattalin arzikinta a shekarar 2024 da ta gabata, wanda alkaluman hakan suka nuna sakamakon jimillar karfin tattalin arzikin kasar na bara, ya kai kudin kasar tiriliyan 134.9, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 18.44, inda adadin ya kai karuwar kaso 5.0 bisa dari kan na shekarar 2023. Tabbas wannan matsayi ya shaida yadda tattalin arzikin kasar ya jure tarin kalubale daban daban, tare da zama manuniya dake tabbatar da irin gudummawar da tattalin arzikin kasar ke ci gaba da baiwa ci gaba mai inganci ga duniya baki daya.
A wannan gaba da duniya ke fama da tafiyar hawainiya wajen farfadowar tattalin arziki, juriyar da tattalin arzikin kasar Sin ya nuna ya zamo wani babban jigo mai daraja, wanda ke samar da gudummawa da ingiza ci gaban sassan tattalin arzikin duniya baki daya.
- Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Arewa Maso Gabashin Kasar Sin Gabanin Bikin Bazara
- Ƙasashe 7 Sun Mara Wa Nijeriya Baya Don Kafa Cibiyar Koyar Da Ilimin Yaɗa Labarai Ta UNESCO – Minista
Sanin kowa ne cewa a halin da ake ciki ana fuskantar matsaloli masu sarkakiya, da tarin kalubale musamman daga sassan wajen kasar Sin, dake fatan ganin kasar ta samu koma baya, amma duk da hakan, Sin ta cimma manyan nasarori a shekarar 2024, inda jimillar darajar sassan tattalin arzikinta ya haura yuan tiriliyan 130 a karon farko a tarihi.
A gani na har kullum kasar Sin na cike da karsashin raya fannonin tattalin arzikinta yadda ya kamata, inda muke ganin yadda kasar ke kara mayar da hankali ga cin gajiya daga sabbin makamashi, da kera ababen hawa masu amfani da lantarki, yayin da take raya dukkanin fannonin bunkasa kai ba tare da gurbata yanayi ba. Wadannan ayyuka da sauran tarin sassan kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha da kasar ke dora muhimmanci a kansu, suna dada shaida yadda Sin ke tafiya da zamani yadda ya kamata.
Bisa tushen tattalin arziki mai karfi, da babbar kasuwar cikin gida, da managarcin tsarin raya masanaantu, Sin na da ikon jure duk wasu kalubale da matsalolin da duniya ke fuskanta a halin yanzu.
Ga wanda ya samu zarafin shiga lunguna da sakon kasar Sin, zai ga yadda kasar ke kokarin cike gibin ci gaba tsakanin birane da yankunan karkara. Inda ake ganin yadda ake aiwatar da karin manufofin raya yankunan karkara kamar yadda ake raya biranen kasar. Hakan ya samar da wani zarafi na samar da wadata ga daukacin sassan kasar Sin bai daya. Kazalika, hakan wata hikima ce ta raya kasa, wadda daukacin alummunta za su ci gajiya ba tare da barin wani sashe a baya ba.
Yayin da Sin ke cimma moriyar raya tattalin arzikinta a dukkanin fannoni, kuma sassan à kasar ke gani a kasa, sauran sassan duniya ma na cin gajiya daga bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, wadda ke matsayin kasa mai tasowa mafi girma a duniya, wadda kuma ke raba fasahohinta na à ci gaba da sauran sassa, mai kuma burin yin tafiyar bai daya tare da daukacin sassan kasa da kasa, ta yadda za a gudu tare a tsira tare.