ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Karrama Sojojinmu Da Suka Sadaukar Da Kai Don Ɗorewar Nijeriya

by Leadership Hausa
1 year ago
Sojojinmu

A duk ranar 15 ga watan Janairu na kowace shekara ne, a Nijeriya, ake gudanar da bikin tunawa da zagayowar ranar dakarun sojujin Nijeriya  mazansu da matansu, ‘yan mazan jiya.

A saboda haka ne, yana da matukar mahammianci mu yi waiwaye kan irin sadaukarwar da suka yi ta rayuwarsu, wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasar, musamman ma idan aka yi la’akari da cewa, sun fafata yakin duniya na daya da na biyu da kuma a lokacin yakin basasar Nijeriya.

  • A Shirye Kasar Sin Take Ta Kyautata Dangantakar Tattalin Arziki Da Amurka
  • Shirin Tallafinmu Ga Nijeriya A 2025 Zai Kai Ga Asalin Mabukata – Wakilin MDD

Ana iya tunawa, kasar Ingila ce, ta reni Nijeriya ta kuma bata ‘yancin kai, a baya ana kara tunawa da zagayowar ranar ce, a ranar 11 na kowane watan Nuwamba, musamman ma domin tuna kawo karshen yakin duniya na farko

ADVERTISEMENT

Sai dai kuma, bayan da waccen Gwamnatin mulkin soji ta samu galaba a kan dakarun sojojin masu yunkurin kafa kasar Biyafara a ranar 15 ga watan Janairun 1970, aka sauya ranar da gudanar da bikin daga cikin Kalandar kasashen renon Ingila wato Commonwealth, zuwa ranar 15 ga watan Janairun domin, a rinka tunawa da yakin na basasa.

Shekaru aru-aru, dakarun sojojin mu, sun sadaukar da rayukansu wajen kare karfin ikon Nijeriya, rayukan ‘yan kasar,  don tabbatar da zaman lafiya da kuma ci gaba da wanzuwar Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Ba Zan Iya Jure Halayen El-Rufai Ba Shi Yasa Na Fice Daga ADC – Salihu Lukman

Kazalika ma, sadaukar da kansu da kwarin gwiwarsu na fuskantar dukkanin wani hadarin yaki, wanda hakan ya sanya aka ci gaba da nuna godiya a gare su, da  kuma girmama su, a daukacin fadin kasar mu.

Hakan ta sa abin ya zama mana wajibi, mu ci gaba da tuna su da kuma girmama su, la’akari da sadaukar da kan da suka yi ga kasar mu.

Hadurun da suka fuskanta, a zahirance suke, in aka tuna da yadda suka rasa rayukansu, wajen yakar ‘yan ta’adda da sauran masu aikata manyan laifuka, da suka zamo barazana, ga tsaron kasar.

Amma a nan, tunanin mu, ya karkata ne, zuwa ga iyalansu da suka rasu suka bari, abokan arzikinsu da kuma yankunan da suka fito.

Bisa sadaukar da rayukansu da suka yi ne, hakan ya sanya muka ci gaba da zama a cikin zaman lafiya muka kuma ci gaba da gudanar da ayyukansu, na yau da kullum.

A saboda haka ne, akwai babban bashi da yake a kanmu, na ci gaba da tunawa da su, tare da kuma girmama su.

A yayin da muke gudana da bikin tuna su, ya zamar mana wajibi mu taimakawa sauran dakarun ‘yan mazan jiya da ke raye da kuma sauran dakarun da a yau, suke ci gaba da nauyin ba  Nijeriya kariya.

Bugu da kari dakarun namu suna ci gaba dayin aiki tukuru wajen tunkarar dukkan wata barazana daga wurin ‘yan ta’adda, ‘yan fashin daji, masu satar danyen mai da sauran masu aikata manyan laifuka, a kasar.

Abin jin dadi ne, matuka, musamman irin dimbin ci gaban da ake ci gaba da samu, musamman yadda, rundunar tsaron kasar ta ruwaito cewa, dakarunta da ta tura masu dakile aikata ta’addanci, a wasu ayyukan da suka kaddamar, sun kashe ‘yan ta’adda 109, tare da kuma cafke wasu 81 a makon farko na 2025.

Daraktan sashen yada labarai na rundunar Manjo Janar Buba Edward, ya sanar da cewa, “A cikin makon dakarun sun hallaka ‘yan ta’adda 109 tare da kama wasu 81 da kuma ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa da su 43.”

Sai dai, a bisa ra’ayin wannan jaridar, duk a wannan dimbin nasarorin da aka samu, akwai sauran manyan kalubale.

Wasu rahotannin suna bayyana cewa, akalla mutane 77 ne, aka kashe tare da kuma yin garkuwa da mutane 43, hakan ya biyo bayan hare-hare da aka kai daban daban a jihohi 10, a cikin mako biyu kacal, da suka wuce.

An kuma kone gidaje da dama, tare da tarwatsa mutane sama da 1,000, daga matsugunansu.

Bugu da kari kuma wasu dakarun soji shida, sun rasa rayukansu, a wani harin na ‘yan ta’adda, a ranar 4 ga watan Janairu 2025.

Sun rasa rayukansu ne, a yayin da maharan suka kai hari a sansanin soja da ke a Sabon Gida, Damboa a jihar Borno.

Bayan kai wannan harin, Shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayar da umarnin da a gudanar da cikakken bincike, tare da kuma yabawa rundunar sojojin kasar kan daukar matakin gaggawa da ta yi, musamman wajen kai hare-hare da Jiragen yaki na sama a kan sansanin ‘yan ta’adda, wanda hakan ya janyo aka kashe su  da dama.

Dole ne mu rinka bai wa dakarun sojojin mu kariyar da ta kamata da kuma kulawa da jin dadinsu da walwalarsu da kula da kiwon lafiyarsu tare da kuma biyan bukatun  iyalansu.

Jajirtattun sojojin da suka dawo daga fagen daga/fama,dole ne a samar masu da gidaje, samar masu da damar samun daukar aiki, domin a karrama su, bisa gudunmawar da suka bayar ta sadaukar da kansu,wajen dorewar tsaro da wanzuwar kasar Nijeriya.

Sojojinmu
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

MASU ALAKA

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Manyan Labarai

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai
Siyasa

Ba Zan Iya Jure Halayen El-Rufai Ba Shi Yasa Na Fice Daga ADC – Salihu Lukman

July 16, 2026
M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin  Mataimakinsa
Manyan Labarai

M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin Mataimakinsa

July 16, 2026
Next Post
Badakalar Tashar Lantarkin Mambilla: Buhari Da Obasanjo Sun Ba Da Shaida A Kotun Duniya

Badakalar Tashar Lantarkin Mambilla: Buhari Da Obasanjo Sun Ba Da Shaida A Kotun Duniya

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

July 16, 2026
Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan

July 16, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai

An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai

July 16, 2026
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai

Ba Zan Iya Jure Halayen El-Rufai Ba Shi Yasa Na Fice Daga ADC – Salihu Lukman

July 16, 2026
Ra’yin Sin Da Afirka Ya Zo Daya A Fannin Fasahar AI

Ra’yin Sin Da Afirka Ya Zo Daya A Fannin Fasahar AI

July 16, 2026
Duk Da Sauye-Sauyen Tattalin Arziƙi Kashi 79% Na Ƴan Nijeriya Na Cikin Talauci – Bankin Duniya

Duk Da Sauye-Sauyen Tattalin Arziƙi Kashi 79% Na Ƴan Nijeriya Na Cikin Talauci – Bankin Duniya

July 16, 2026
M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin  Mataimakinsa

M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin Mataimakinsa

July 16, 2026
Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

July 16, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta

Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta

July 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.