Ya zuwa karshen shekarar 2023 da ta gabata, kasar Sin na da kananan jirage marasa matuka sama da miliyan 1.26, adadin da ya karu da kaso 32 bisa dari a shekara, kamar yadda hukumar lura da sufurin sama na farar hula ta kasar ko CAAC ta bayyana.
Alkaluman CAACn sun nuna cewa, a shekarar da ta gabata, tsawon lokacin zirga-zirgar wadannan jirage ya wuce sa’o’i miliyan 23. Kaza lika hukumar ta amince da kafa yankunan gwajinsu har 17, da sansanonin gwaji 3, wadanda suka shafi yankunan birane, da tsibirai, da wasu sassa masu nasaba da ayyukan jiragen.
- An Bude Sabon Shafin Internet Na Samar Da Hidimomi Na Kasa Da Kasa Na Beijing
- Damarmaki Suna Kasar Sin
A cewar kwararru, kara yawaitar irin wadannan jirage dake zirga-zirga a Sin, da kafa yankunan gwajinsu, na nuni ga yadda sashen tattalin arzikin fannin, da masana’antu masu alaka da shi ke fadada.
Jami’an ma’aikatar raya masana’antu da fasahar sadarwa na Sin sun bayyana cewa, masana’antun zirga-zirgar sama na farar hula, ginshiki ne na tattalin arziki mai nasaba da sufurin ababen hawa masu tafiya a sama maras nisa, wanda ke dogaro da kirkire-kirkire, da ba da misalin amfani da jirage masu nasaba, a kokarin gaggauta sabunta fasahar zirga-zirgar sama na farar hula, da kuma injuna, da kirkiro sabuwar hanyar raya masana’antun zirga-zirgar sama na farar hula mai sigar musamman ta kasar Sin. (Saminu Alhassan)