Kasar Sin za ta iya taka muhimmiyar rawa cikin ajandar Masar ta bunkasa ayyukan masana’antu daga shekarar 2024-2030.
Mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Masar Mohamed Abou El-Enein ne ya bayyana haka jiya Asabar, yayin tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a gefen taron tattaunawa kan tattalin arziki na Akhbar El Youm karo na 11, a birnin Alkahiran Masar.
- Haƙar Ma’adanai Na Sa Yara Ficewa Daga Makaranta A Jos
- Akwai Arzikin Duniya Da Na Lahira A Harkar Fim- Malam Inuwa
Mohamed El-Enein ya ce kasar Sin muhimmiyar abokiyar hulda ce a bangaren masana’antu, kuma za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Masar a wannan bangare.
Ya kuma yaba da goyon bayan da Sin ke ba Masar a dukkan bangarorin masana’antu, yana mai cewa, manyan kamfanonin Sin da dama na aiki a Masar, inda suke bayar da gudunmuwa ga tattalin arzikin kasar.
Ya ce yana fata hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu zai fadada a fannin fasahohin da suka shafi makomar masana’antu da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI, ta yadda zai bayar da gudunmuwa ga bunkasa tattalin arzikin Masar a kowane bangare.
Bugu da kari, jami’in ya ce Sin na taimakawa Masar wajen kafa masana’antar samar da ababen hawa a cikin gida, ta hanyar kafa irin wadannan masana’atu a kasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)