Yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya gudanar da taron manema labarai da aka saba yi yau da kullum.
Da yake tsokaci game da yadda Sin ta aika wa hukumomin da abin ya shafa na MDD rahotonni guda biyu a kwanan baya, domin gabatar da sakamakon da Sin ta samu yayin tinkarar sauyin yanayi, Guo Jiakun ya ce, rahotannin guda biyu sun nuna aniyar kasar wajen yaki da sauyin yanayi, kuma Sin na fatan kiyaye duniyar da bil’adama ke rayuwa tare da samun bunkasar ci gaba mara gurbata muhalli.
- Me Ya Sa “TikTok Refugee” Na Amurka Suke Ta Kama REDnote Ta Kasar Sin
- Hisbah Ta Yi Kakkausan Gargaɗi Tare Da Kira Ga Iyaye Kan Kula Da Yara Bayan Samun Gawar Wasu 4
Dangane da yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas a Gaza kuwa, Guo Jiakun ya ce, Sin na maraba da hakan, kuma tana fatan za a iya aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.
Da ya juya kan kalaman Amurka da suka shafi yankin Taiwan, Guo Jiakun ya bayyana cewa, kamata ya yi Amurka ta daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin kan batun yankin Taiwan.
Haka nan a game da yunkurin Amurka na yin katsalandan a harkokin Hong Kong, Guo Jiakun ya ce, duk wani yunkuri na yi wa Hong Kong batanci ba zai yi nasara ba.
A kan batun kamawa da yanke hukuncin da aka yi wa wasu ‘yan kasar Sin uku a jamhuiryar demokuradiyar Kongo, bisa laifin mallakar sandunan zinari da tsabar kudi da yawa kuwa, Guo Jiakun ya ce, a ko da yaushe gwamnatin kasar Sin tana tsawatar wa ‘yan kasarta dake ketare a kan bin dokokin kasashen da suke, kana ta yi fatan Kongo za ta gudanar da shari’ar bisa doka da adalci, a sa’i daya kuma tare da kare halasci da hakki da kuma moriyar Sinawa.(Safiyah Ma)