Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce kasar na fatan dukkanin sassan masu ruwa da tsaki a Jamhuriyar Nijar za su warware sabanin dake tsakanin su ta hanyar komawa teburin shawara, kana su gaggauta maido da doka da odar.
Kakakin wanda ya bayyana matsayar kasar Sin, yayin da aka tambaye shi game da halin da ake ciki a Nijar, ya ce Sin na nazartar yanayin yadda ya kamata, ta kuma lura da kalaman da suka fito daga MDD, da kungiyar ECOWAS.
Kakakin na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana shugaban da sojoji suka yiwa juyin mulki a Nijar Mohamed Bazoum, a matsayin aboki ga kasar Sin, kuma Sin din na fatan za a tabbatar da kare lafiyar sa, kana sassan masu ruwa da tsaki a kasar za su sanya kare moriyar kasar da al’ummar ta gaban komai.
Kaza lika, jami’in ya ce Sin na burin ganin an warware takaddamar da ake yi ciwon ruwan sanyi ta hanyar tattaunawa, a kuma gaggauta dawo da doka da odar, tare da ingiza daidaito da ci gaban kasar ta Nijar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp