Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau cewa, a shekarun baya-baya nan, an gwada sabbin kayayyayin fasahohin zamani kamar mutum-mutumin inji mai siffar dan Adam, da gilas na zamani, da na’urorin ba da jinya dake hade da kwakwalwa da inji da sauransu, a dandalin bikin baje koli na kayayyakin shige da fice na Guangzhou wato Canton Fair, da bikin baje koli na kayayyakin sayayya na kasa da kasa, da bikin baje koli na kayayyakin da ake samarwa na kasa da kasa wato CISCE da sauransu.
Wadannan bukukuwan baje koli sun shaida sabon karfin Sin na samar da hajoji da hidimomi masu karko, kana sun kasance muhimmin gadar dake hade sassan kasa da kasa kan mu’amalar kimiyya da fasahohi, ko hakan ya shaida tunanin kasar Sin na raya fasahohi, da yin kirkire-kirkire mai bude kofa ga kowa, da samun moriyar juna.
Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin ta gudanar da kirkire-kirkire don raya kanta, har ma da samar da moriya ga dukkanin duniya baki daya. Sin tana kuma fatan yin kokari tare da sauran sassan kasa da kasa wajen sa kaimi ga raya fasahohin zamani, ta hanyar hadin gwiwa da bude kofa, da ci gaba da zamanintar da kasashen duniya, ta hanyar yin kirkire-kirkire. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp