Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana a yau Talata 24 ga wata cewa, tun barkewar rikicin Palestinu da Isra’ila a wannan zagaye, kasarta na kara tuntubar bangarori masu ruwa da tsaki, da nuna kwazo wajen halartar shawarwarin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, da taimakawa ga samun sulhu da neman mafita. Kasashen duniya, musamman kasashen Larabawa sun yaba da matsayin kasar Sin gami da muhimmiyar rawar da ta taka.
Mao ta ce, kasar Sin da kasashen Labarawa sun cimma matsaya daya kan kazamin fadan da a yanzu haka ake yi tsakanin Palestinu da Isra’ila, inda ta ce, muna fatan za’a tsagaita bude wuta ba tare da wani jinkiri ba, don kar yanayi da ake ciki ya kara tabarbarewa, kuma muna adawa da duk wani yunkuri na illata fararen-hula da abun da ya sabawa dokokin kasa da kasa, muna kuma goyon-bayan “shirin kasantuwar kasashe biyu”, da baiwa Palesdinawa hakkokin kafa kasa, da rayuwa da dawowa matsugunansu, wannan ita ce mafitar da ka iya daidaita batun Palestinu.
Jami’ar ta kara da cewa, muna goyon-bayan gudanar da wani taron neman sulhu wanda ya shafi karin kasashe kuma mai kwarjini tun da wuri, da gaggauta farfado da shawarwari tsakanin Palestinu da Isra’ila, tare kuma da kafa ajanda da taswira kan wannan batu. (Murtala Zhang)