Kasar Sin na hasashen samun karin yabanyar hatsi a shekarar nan ta 2025, da adadin da zai dara na bara wato tan miliyan 706.5, yayin da ake kara karfafa ikon kasar na samar da hatsi da sauran nau’o’in amfanin gona.
Wani rahoton da kwamitin nazarin albarkatun gona karkashin ma’aikatar noma da raya karkara ta kasar ta fitar jiya Lahadi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa bisa hasashen a shekarar ta bana, adadin hatsin da za a girba a kasar zai kai tan miliyan 709, kuma hakan na da nasaba da karin kwazon da ake yi na kara yawan yabanyar da kowane nau’in hatsi ke samarwa, da fadadar himmar shuka nau’o’in hatsi daban daban da kuma sarrafa su.
Rahoton ya kara da cewa bisa hasashen, a bana adadin waken soya da za a girba a kasar Sin zai karu da kaso 2.5 bisa dari kan na shekarar bara, inda zai kai tan miliyan 21.17.
Har ila yau, rahoton ya nuna cewa, yayin da adadin yabanya ke karuwa a cikin gida, kuma karuwar bukatunsu ke raguwa, akwai hasashen raguwar bukatar shigo da nau’o’in amfanin gona cikin kasar daga ketare. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp