Hukumar dake lura da ikon mallakar fasahohi ta kasar Sin, ta ce a shekarar 2022, kasar ta samu karuwar yawa, da ingancin shaidun mallakar fasahohin kirkire-kirkire. A cewar shugaban hukumar Shen Changyu, a shekarar ta bara, an ba da shaidun mallakar fasahohi har 798,000, adadin da ya nuna karuwar neman ikon mallakar manyan fasahohi a kasar zuwa mutum 9.4 cikin duk mutum 10,000. Shen ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da ya gudana a Litinin din nan a birnin Beijing.
Wasu alkaluma da ma’aikatar ilimi ta kasar Sin ta fitar a watan Mayun bara, sun nuna yadda manufofin kasar a fannin ingiza cin gajiya daga basirar kirkire-kirkire suka taimakawa kasar matuka.
Karkashin manufofin, Sin ta kafa managarcin tsarin samar da ilimi a matakin jami’a mafi girma a duniya, inda ‘yan kasar miliyan 240 ke samun ilimi a irin wadannan makarantu, cikin jimillar ‘yan kasar biliyan 1.4. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)