Hukumar samar da bunkasa da hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin ta gabatar da taron manema labarai a yau Juma’a, inda aka yi karin haske game da yadda Sin take baiwa kasashen Afirka tallafi da samun bunkasa tare da su cikin hadin gwiwa.
An ce, ya zuwa yanzu, Sin tana taimakawa kasashen Afirka fiye da 21 a bangaren kimiyyar aikin gona, inda ta tura musu kwararrun aikin gona fiye da 200. Kazalika, bangarorin biyu suna hadin gwiwa wajen gudanar da ayyukan dake da nasaba da na’urorin wutar lantarki da horar da kwararru da habaka da karfinsu da sauran bangarori. Kana suna kaddamar da ayyukan samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, ciki har da samar da wutar lantarki ta amfani da karfin ruwa, da na hasken rana da samar da ruwa da sauransu.
Ban da wannan kuma, Sin ta taimaka wa kasashen Afirka wajen kara karfinsu na samun bunkasa. Kana ta riga ta horar da kwararrun ’yan Afirka fiye da dubu 15 tun bayan kiran taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da aka gudanar a bara a birnin Beijing. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp