Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a ranar 6 ga watan nan cewa, shaharar da kallon fina-finai na lokacin hutu na Bikin Bazara na al’ummar Sinawa ya yi manuniya ce a kan dimbin albarkar da kasuwar masarufi ta kasar Sin ke da ita, da karfin kasar na raya tattalin arziki, da kuma kyakkyawar makomar bunkasar tattalin arzikin kasar ta Sin. Saboda haka, kasar Sin tana lale marhabin da baki daga daukacin fadin duniya su zo su ga kyawawan al’adun Sinawa tare da more wa abin.
Kididdiga ta nuna cewa, ya zuwa ran 5 ga watan Fabrairu, adadin kudin da aka samu na tikitin kallon fina-finai a lokacin hutun Bikin Bazarar, ya zarce Yuan biliyan 10, kuma masu kallon fina-finai sun kai yawan miliyan 187, wanda ya zama adadi mafi kololuwa da aka samu. Kazalika, an fitar da fina-finai da dama zuwa kasashen waje a lokaci guda, inda kuma wasu suka kasance kan gaba a gidajen sinima da ake kallon fina-finan da ba na Ingilishi ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)