Yau Litinin, an gudanar da taron shigo da jarin waje daga dukkan sana’o’i a tashar ciniki maras shinge ta Hainan na shekarar 2025 a birnin Haikou, hedkwatar lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.
Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng ya halarci taron tare da gabatar da jawabi, inda ya ce yanzu haka Hainan ya zama wani dandali mafi rinjaye a nan kasar Sin a fannin bude kofa ga ketare, kuma wuri da ya fi jawo hankalin masu zuba jari, da mafiya karfin hadin gwiwar shiyya-shiyya, kana mai ingiza matakin gaggauta dunkulewar tattalin arzikin duniya.
- Mafarauta Sun Nemi Adalci Kan Kisan Mambobinsu A Edo
- Sojoji Sun Ceto Fasinjoji 16 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Filato
Han ya kara da cewa, Sin na nacewa ga tsarin bude kofarta ga ketare, da kuma gabatar da damammakinta na bunkasuwa ga sauran sassa, kana da ci gaba da baiwa kamfanonin kasa da kasa wani dandali mai kyau na samun bunkasa.
Dadin dadawa, Sin za ta ci gaba da shimfida yanayin ciniki mai inganci, da samarwa kamfanonin ingantattun hidimomi. Sin na maraba da masu zuba jari na sassan duniya da su gudanar da hada-hadarsu a kasar musamman ma wannan tasha ta ciniki maras shinge da more zarafin ci gaban Sin tare. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp