Ofishin wakilcin hada-hadar cinikayya na kasar Amurka, ya sanar da kwaskwarimar karin haraji kan hajojin kasar Sin dake shiga Amurka, karkashin kudurin dokar nan mai lamba 301.
A jiya Asabar, cibiyar bunkasa hada-hadar cinikayya ta kasa da kasa ta Sin CCPIT, ta ce matakin kashin kai na Amurka, wanda ya sabawa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, ya yi matukar illata kwarin gwiwar sassan Sin da Amurka ta fuskar hadin gwiwa na dogon lokaci, tare da gurgunta tsarin rarraba hajoji na kasa da kasa da kuma tsarin masana’antu na kasa da kasa.
- Shugaban Zambia: Kudurorin Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Da Sin Ta Gabatar Za Su Bunkasa Nasarar Hadin Kan Sassan 2
- An Yi Bikin “Rubutu A Samaniya: Labari Na A Kasar Sin” Na Murnar Cika Shekaru 75 Da Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin A Jamus
Kaza lika, a cewar kakakin cibiyar CCPIT, gungun sassan ‘yan kasuwa na Sin, sun bayyana matukar adawarsu da matakin na Amurka.
A daya bangaren kuma, CCPIT da hukumar bunkasa cinikayyar kasa da kasa ta Sin, sun jima suna kokarin yaukaka hadin gwiwa tsakanin ‘yan kasuwar sassa daban daban na duniya. Kuma a wannan karo ma suna kira ga gwamnatin Amurka da ta martaba dokokin kasuwa, da kyakkyawan yanayin takara, ta kuma dakatar da daukar miyagun matakai, ta rungumi ka’idojin gudanar da cinikayya na kasa da kasa karkashin tanade-tanaden kungiyar WTO. (Saminu Alhassan)