Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyanawa taron manema labaru da aka saba shiryawa Alhamis din nan cewa, duk wasu karairayi da jita-jita masu nasaba da jihar Xinjiang ta kasar Sin, gaskiya za ta yi halin ta, kuma yunkurin da wasu kasashe ke yi na neman bata sunan kasar, ta hanyar amfani da wasu batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang ba za su taba yin nasara ba.
An bayar da rahoton cewa, kimanin kungiyoyi masu zaman kansu na gida da wajen kasar Sin dubu 1 ne, suka aike da wasikar hadin gwiwa ga babbar jami’ar kare hakkin dan-Adam ta MDD Michelle Bachelet, domin nuna adawarsu game da rahoton da ofishin ya fitar kan jihar Xinjiang.
Zhao Lijian ya jaddada cewa, kasar Sin tana kira ga hukumar OHCHR, da ta mutunta babban damuwar jama’ar kasar Sin da dukkan mutane masu sanin ya kamata a duniya, da tsayawa kan bangaren tarihi, da kin wallafa rahotannin da suka shafi jihar Xinjiang ta kasar Sin bisa bayanan karya da kuma zarge-zarge.(Ibrahim)