A jiya Litinin, firaministan kasar Sin, Li Qiang ya jagoranci taron zartaswa na majalisar gudanarwar kasar, wanda ya zayyana matakan da za a dauka don bunkasa harkokin sayayyar abubuwan bukata a cikin gida, tare da amincewa da shirin daidaita zuba jarin waje a shekarar 2025.
Taron ya yi kiran ba da tallafi mai karfi don kara yawan kudin shiga na magidanta, da habaka karin albashi mai ma’ana, da kuma inganta karfin al’umma na sayen abubuwan bukata.
- Gwamna Nasir Ya Sauke Sakatarorin Hukumar Ilimi Na Kananan Hukumomi 21 A Kebbi
- Abin Kunya Ne Nijeriya Har Yanzu Ba Ta Iya Ciyar Da Kanta – Gwamna Bala
Ya jaddada muhimmancin mayar da hankali kan sassan sayen kayayyaki da ke da tasiri mai karfi da za su iya kawo katafaren ci gaban da za a ci gajiyarsa wajen bunkasa harkokin sayen kayayyaki.
Har ila yau, taron ya bayyana muhimmancin fadada amfani da bangaren al’adu, da wasanni da yawon bude ido.
Kazalika, taron ya kuma bayyana cewa, kamfanonin kasashen waje suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi, da daidaita fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, da inganta masana’antu, kana ya bukaci a kara azama, da samar da ingantattun matakai domin daidaita zuba jarin kasashen waje da ake da su da kuma fadada samun wasu sabbi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)