Hukumomin kwastam na kasar Sin sun bayyana Talatar nan cewa, kasar ta samar da karin damar shiga kasuwannin shigo da kayayyakin amfanin gona da na abinci, daga kasashe da yankuna sama da 51 a shekarar 2023.
A cikin wata sanarwa da babbar hukumar kwastam ta kasar ta fitar ta bayyana cewa, amincewa da jigilar nau’o’in kayayyakin gona da na abinci 146 da ake shigowa da su daga kasashen waje, ya taimaka wajen biyan bukatun al’ummar Sinawa, da kuma burinsu na samun ingantacciyar rayuwa.
A cewar sanarwar, babbar hukumar kwastam ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwarta da ragowar kasashen duniya a shekarar 2023. Ta kuma sanya hannu a kan jimillar takardun hadin gwiwa 156 tare da abokan huldar kasashen waje, ciki har da takardu 84 kan yadda kayayyakin amfanin gona da na abinci, za su samu damar shiga kasuwanni tare da abokan huldar hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya. (Mai fassara: Ibrahim)