A yau Alhamis ne kasar Sin ta bayyana sakamakon kidayar harkokin tattalin arzikinta karo na biyar wanda ya nuna cewa tattalin arzikin kasar ya samu ci gaba, yayin da kuma yake tafiya a kan kyakkyawar turba ba tare samun cikas ba a shekaru biyar da suka gabata.
Sakamakon kidayar ya nuna cewa, Sin ta yi rajistar masana’antun kere-kere da na hidimomi miliyan 33.27 zuwa karshen shekarar 2023, inda abin ya bunkasa da kashi 52.7 idan aka kwatanta da na karshen shekarar 2018.
Wadannan masana’antun sun dauki ma’aikata fiye da miliyan 428.98 zuwa karshen 2023, inda aka samu karin yawan ma’aikatan da aka dauka da kashi 11.9 cikin dari, idan aka kwatanta da na karshen shekarar 2018. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp