Gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da ofishin jakadancinta a Honduras a jiya Litinin, bayan da kasashen biyu suka kulla huldar diflomasiyya tsakanin su a ranar 26 ga watan Maris.
Yayin bikin kaddamarwar, mukaddashin jakada a ofishin Yu Bo ya ce Honduras ta yi amfani da kyakkyawar dama a tarihi, wajen aiwatar da muhimmin mataki na amincewa da ka’idar kasar Sin daya tak a duniya.
Yu Bo ya kara da cewa, da wannan mataki, Honduras ta zama kasa ta 182 a jerin kasashen da suka kulla huldar jakadanci da kasar Sin, matakin da kasar ta Sin ta yi matukar yabawa.
Yayin da yake halartar taron kaddamarwar, ministan harkokin wajen Honduras Eduardo Reina, ya jaddada cewa, kulla dangantakar jakadanci da kasar Sin zabi ne na kashin kai da Honduras ta amincewa.
Kuma hakan ya fadada alakar kasar da sauran sassan duniya, tare da hade kasar da sauran kasashen duniya da suka amince da kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.
Reina ya kara da cewa, a wannan gaba da Honduras ta amince da wannan manufa, a daya hannu ta shirya tsaf domin gudanar da hadin gwiwar cinikayya tare da Sin, da nufin bunkasa kayayyakin more rayuwa, da bunkasa rayuwar al’ummar Honduras da samar da wadata. (Saminu Alhassan)