A yau Laraba, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin tana adawa da duk wani nau’i na mu’amala a hukumance tsakanin Amurka da yankin Taiwan na kasar Sin, inda ta bukaci Amurka da ta dakatar da cudanya a hukumance a tsakaninta da Taiwan, da kuma kaurace wa yi wa ‘yan aware “masu neman ‘yancin Taiwan” ingiza mai kantu ruwa.
An ba da rahoton cewa, shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan wata doka da ta bukaci ma’aikatar harkokin wajen kasar da ta rika yin nazari a-kai-a-kai game da mu’amalar da ke tsakanin Amurka da Taiwan, da kuma neman hanyoyin zurfafa hulda da Taiwan.
Da yake mayar da martani, Lin Jian ya shaida wa taron manema labarai da aka saba gudanarwa a-kai-a-kai cewa, batun yankin Taiwan babban jigo ne a cikin muradun kasar Sin, kuma iyaka ce da ba za a iya ketarewa ba a huldar da ke tsakanin Sin da Amurka. Don haka, kasar Sin ta bukaci Amurka ba tare da wani bata lokaci ba ta mutunta ka’idar Sin daya tilo a duniya da kuma sanarwar hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurkar suka fitar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














