Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakai na kare halastattun moriyarta bisa doka.
Mao Ning ta yi tsokacin ne, yayin da take mayar da martani game da kalaman kakakin hukumar tsaron Amurka ta Pentagon John Kirby, wanda aka jiyo shi yana cewa, kasar sa ba za ta mika sassan kumbon nan maras matuki na farar hula da ta harbo ga kasar Sin ba.
Mao ta jaddada cewa, ba da gangan kumbon ya shiga samaniyar Amurka ba, hakan ya faru ne bisa kuskure, cikin yanayi da ba a yi tsammani ba. Kaza lika kumbon ba shi da wani hadari ga jama’ar Amurka ko tsaron kasar.
Jami’ar ta ce kamata ya yi Amurka ta shawo kan lamarin ta hanyar kai zuciya nesa, da nuna kwarewa ba tare da amfani da karfin soji ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp