Kasar Sin ta bukaci Amurka ta daina samarwa Taiwan makamai nan take, kuma ta dakatar da aikata ayyuka masu hadari dake kawo tsaiko ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ne ya bayyana hakan a jiya Asabar, yayin mayar da martani ga tambayar wani dan jarida game da sanawar ma’aikatar tsaron Amurka cewa, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta amince da sayar da makaman da darajarsu ta kai dala biliyan 1.988 ga Taiwan, ciki har da kayayyakin yaki na sa ido da masu kakkabo makamai masu linzami daga sararin samaniya.
- Kotu Ta Dakatar da JAMB Daga Hana Ɗalibai Ƴan Ƙasa Da Shekaru 16 Shiga Jami’a
- NNPP Ta Lashe Kujerun Shugabannin Kananan Hukumomi 44 Da Kansiloli 484 Na Jihar Kano
A cewar kakakin, shirin sayar da makamai ga Taiwan ya take manufar kasancewar Sin daya tak a duniya da kuma sanarwoyin hadin gwiwa 3 dake tsakanin Sin da Amurka, musammam sanarwar ranar 17 ga watan Augustan 1982.
Ya kara da cewa, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba na tabbatar da kare cikakken ‘yancinta da ikonta kan yankunanta da kuma tsaron kasa. (Fa’iza Mustapha)