A yayin taron manema labarai na yau da kullum da ya gudana a yau Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya amsa tambayoyi dangane da batun asalin cutar COVID-19.
Jami’in ya soki wasu shafukan intanet na Amurka saboda farfado da batun nan na “tonon asirin dakin bincike” ba tare da wata sahihiyar hujja ba, yana mai cewa hakan ba komai ba ne illa tuhume-tuhume marasa tushe da kuma nuna ha’incin siyasa da nufin shafa wa kasar Sin kashin kaji.
- 2027: Fastocin Takarar Shugaban Ƙasa Na Gwamnan Bauchi Sun Bayyana
- Tinubu Ya Komo Nijeriya Bayan Ziyarar Mako 3 A Turai
Ya bayyana cewa, kasar Sin tana ci gaba da nuna adawa da irin wannan munakisa, yana mai jaddada cewa gano asalin kwayar cutar wani lamari ne mai tsananin sarkakiyar kimiyya.
Guo Jiakun ya kara da cewa, kasar Sin ta kiyaye amfani da tsarin kimiyya da babu rufa-rufa a ciki mai baje komai a faifai, tare da nuna goyon baya da kuma shiga cikin kokarin da kasashen duniya ke yi na gano ainihin inda cutar ta samo asali.
Ya bukaci Amurka da ta daina siyasantar da lamarin, da amfani da batun gano asalin cutar a matsayin makami, kana ya nemi Washington ta guji yin kafar ungulu ga wasu kasashe, da dora wa wasu laifi, da yin watsi da tababar da ake ta nunawa a game da ayyukanta masu nasaba da cutar. Kazalika, ya jaddada bukatar ganin Amurka ta warware matsalolin da kasashen duniya suka nuna damuwa a kai tare da bayar da cikakken gamsasshen bayani a kan lamarin ga al’ummar duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp