Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, He Yongqian, ta bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka ta dakatar da matakan kakaba harajin da ta dauka bisa binciken sashe na 232 ba tare da wani bata lokaci ba.
A yayin taron manema labaru na yau da kullum, jami’ar ta ce, harajin kwastam na sashe na 232 da aka kakaba wa motocin da ake shigar da su daga waje, da karafa, da holoko, da kuma binciken sashe na 232 kan magunguna, “zallar aiki ne na mamayar bangare daya da kuma kariyar cinikayya.”
Jami’ar ta kara da cewa, kasar Sin ta yi kira ga Amurka da ta gaggauta kawo karshen matakan harajin na sashe na 232, tare da magance korafe-korafen dukkan bangarori yadda ya kamata, ta hanyar tattaunawa bisa daidaito. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














