• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Bukaci Isra’ila Ta Janye Daga Yankunan Palasdinu Da Ta Mamaye

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 year ago
Sin

Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga Isra’ila da ta saurari kiran da kasa da kasa ke yi mata, na ta janye nan take daga yankunan Palasdinu da ta mamaye.

Da yake tsokaci yayin wani zama na musamman game da batun Palasdinu, Fu Cong ya bayyana cewa, kawo karshen mamayar na nufin shawo kan rashin adalcin da aka dade ana yi, kuma abu mafi muhimmanci shi ne, shimfida tubalin zaman lafiya.

  • Lagdo Dam: Akwai Yiwuwar Jihohi 11 Su Fuskanci Ambaliya A Nijeriya
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 4 A Birnin Gwari Da Giwa Bayan Kuɓutar Da Mutane 20 

Ya kuma jaddada cewa, kafa ‘yantattun kasashe biyu, ita ce kadai hanyar warware batun Palasdinu, kuma ita ce matsayar da kasashen duniya suka cimma.

A cewarsa, kasar Sin na kira da a kira babban taron kasashen duniya kan zaman lafiya, domin farfado da damarmaki a siyasance, na kafa kasashe biyu da kuma tsara jadawali da hanyar aiwatar da shi.

Ya kara da cewa, Palasdinu ta samu kujera tsakanin mambobin MDD, kuma ta gabatar da wani kuduri gaban zauren majalisar, wanda ke neman ya mayar da hankali wajen aiwatar da shawarar da kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya (ICJ) ta bayar.

LABARAI MASU NASABA

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

Bugu da kari, wakilin na Sin ya ce kasarsa za ta kada kuri’ar amincewa da kudurin, kuma tana fatan kudurin zai samar da sabon kuzarin kawo karshen mamayar da kafa ‘yantattun kasashe biyu, da kuma daukaka tsarin wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba
Daga Birnin Sin

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

October 13, 2025
Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta
Daga Birnin Sin

Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

October 13, 2025
Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin
Daga Birnin Sin

Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

October 13, 2025
Next Post
Bidiyon Dalar Ganduje: Kotu Za Ta Yanke Hukunci Ranar 22 Ga Satumba 

Kotu Ta Sanya Rana Kan Batun Tsige Ganduje A Matsayin Shugaban APC

LABARAI MASU NASABA

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

October 14, 2025
Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

October 13, 2025
Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

October 13, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

October 13, 2025
Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

October 13, 2025
NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3

NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3

October 13, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

October 13, 2025
Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

October 13, 2025
Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA

Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA

October 13, 2025
Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba

Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba

October 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.