Kasar Sin ta bukaci Japan da ta janye mummunar shawarar da ta yanke ta zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum Talatar nan cewa, Japan ba ta tuntubi ragowar kasashen duniya ba, musamman masu ruwa da tsaki kan shirinta na zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku.
A ranar 24 ga watan Agusta ne dai Japan za ta fara zubar da gurbataccen ruwan da aka adana a tashar makamashin nukiliya ta Fukushima Daiichi zuwa cikin tekun, kamar yadda Firaministan Japan Fumio Kishida ya sanar a yau.
Wang ya bayyana cewa, Japan ta nuna son kai matuka, da rashin da’a wajen mika hadarin gurbacewar makamashin nukiliya ga duniya, tare da fifita muradunta sama da lafiyar dukkan daukacin bil Adama. Kuma a cewarsa Sin ta damu matuka kuma tana matukar adawa da wannan mataki, ta kuma gabatar da kokenta ga bangaren Japan.(Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp