Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gabatar da korafi mai tsanani ga Japan, dangane da munanan kalaman da take yi game da katafaren taron da kasar Sin za ta yi, albarkacin cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa ta yi nasara a yakin kin harin Japan da yakin duniya na II.
Yayin taron manema labarai na yau Talata, kakakin ma’aikatar Guo Jiakun, ya ce manufar tunawa da ranar ita ce, tunawa da tarihi da kuma girmama zaman lafiya.
Ya ce duk wata kasa da za ta kalli tarihin da daraja tare da daukar darasi, kuma take da burin neman ci gaba cikin lumana, ba za ta ki amincewa da shi ba.
Ya ce fahimtar tarihi da daukarsa yadda ya kamata, muhimmin tubali ne na komawar Japan cikin harkokin kasa da kasa bayan yakin, kuma shi ne tubalin siyasa na raya dangantakarta da kasashe makwabta, haka kuma muhimmin ma’auni ne na gwada ko Japan za ta cika alkawarinta na neman ci gaba cikin lumana.
Kakakin ya bukaci Japan da ta fuskanci tarihin ta kuma nazarci kutsen da ta yi, ta ajiye batun kara karfinta na soji a gefe, ta bi tafarkin neman ci gaba cikin lumana da girmama abun da ke zukatan al’ummar Sinawa da sauran kasashen da lamarin ya shafa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp