A baya-bayan nan ne ministan ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin Yin Hejun da kwamishinan AU mai lura da harkokin ilimi, kimiyya da kirkire-kirkiren fasaha, Gaspard Banyankimbona, suka sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, a madadin gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kungiyar AU, dangane da hadin gwiwar raya bangaren kimiyya da fasaha.
Karkashin wannan yarjejeniya, sassan biyu za su yi hadin kai wajen aiwatar da bincike, da gina dandalin hadin gwiwa na raya fasahohi, da aiwatar da musayar kwarewar fasahohi, da kirkire-kirkire da sana’o’i da sauransu.
Ina matukar taya nahiyar Afrika murna domin wannan abun farin ciki ne gare ta, ganin cewa idan batu ake na kimiyya da fasahar zamani, to dole ne a kira kasar Sin saboda dimbin ci gaban da ta samu da ma yadda take mayar da hankali wajen bincike da kirkire-kirkire da kuma yadda a kusan kullum, masana a kasar ke bullo da sabbin abubuwa na kimiyya da fasaha. Baya ga haka, babu mafi dacewa da ya kamata nahiyar Afrika ta hada gwiwa da ita a wannan fanni da ya wuce kasar Sin, duba da muradinta na ganin an ci gaba tare, an samu moriya tare da kuma yadda take taimakawa ba tare da rufa-rufa ko gindaya sharadi ko ma katsalandan cikin harkokin kasashe ba.
Kasar Sin ta ciri tuta idan ana batu na kimiyya da fasaha. Cikin mizanin kirkire-kirkire na duniya da hukumar kula da hakkin mallaka ta duniya WIPO ta fitar a baya-bayan nan, a karon farko kasar Sin ta shiga jerin kasashe 10 dake kan gaba a fannin kirkire-kirkire, lamarin da ya tabbatar da ci gaban da kasar ke samu da kuma nuna kwalliya ta biyan kudin sabulu daga jajircewarta da manufofi da dimbin jarin da take zubawa bangaren.
Yayin da kasashe masu tasowa suka kasance koma baya, ci gaban kasar Sin zaburarwa ce a gare su cewa, su ma za su iya dogaro da karfinsu, kuma su samu ci gaba. Haka kuma, taimakonta gare su, ba shakka zai taka rawa wajen daga matsayinsu da kwarewarsu a fannin kimiyya da fasaha. Kamar yadda kullum nake fada, ci gaban kasar Sin, ci gaba ne ga kasashenmu na nahiyar Afrika domin duk wata nasara da ta samu, tana son su ma su samu. Don haka, ina ganin wannan hadin gwiwa da AU ta yi da Sin, dama ce ga kasashen Afrika ta kara karfinsu da kwarewa a bangaren ta yadda za su samu ci gaba kuma al’ummominsu su amfana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp