Kwararrun kasar Kenya, sun fitar da wani rahoto a kwanan nan, wanda ya bayyana cewa, binciken jin ra’ayoyin jama’a ya nuna cewa, kasar Sin ta fi kungiyar tarayyar Turai wato EU sauri da aminci, wajen inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma a kasashen Afirka.
Da yake amsa tambayar da aka yi masa game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce tun bayan kafa dandalin FOCAC na tattauna hadin-kan Sin da Afirka, kamfanonin kasar Sin sun shimfida layukan dogo da tsawonsu ya zarce kilomita dubu 10, da hanyoyin mota masu tsawon kilomita kusan dubu 100, tare da gina daruruwan gadoji, da tashoshin jiragen ruwa, da asibitoci, da makarantu da yawa a dukkanin sassan nahiyar Afirka.
Sai dai duk da hakan, wasu mutane na shafawa hadin-gwiwar Sin da Afirka bakin fenti, inda suke kokarin yayata wani ra’ayi dake ganin baiken ”gina muhimman ababen more rayuwar al’umma masu ingancin gaske”.
Sai dai a cewar Wang, mene ne ainihin ababen more rayuwa masu ingancin gaske? Kuma wanene ke iya kokari wajen samar da alheri ga al’ummun kasashen Afirka? Wadannan tambayoyi ne da su al’ummun Afirka kadai za su iya ba da amsar su.
Wang ya jaddada cewa, kasar Sin na ganin cewa, ya dace Afirka ta zama wani babban dandamali, na hadin-gwiwar kasa da kasa, kuma ya kamata kasa da kasa su kara samar da alfanu ga al’ummun Afirka, bisa tushen girmama ‘yancin kansu, da sauraron muryoyinsu. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp