Sashen lura da haraji na hukumar kwastam ta kasar Sin ya sanar da daidaita harajin da Sin ta ayyana kan hajojin Amurka da ake shigarwa kasar tun daga karfe 12:01 na Larabar nan.
Karkashin tsarin da za a aiwatar, Sin ta daidaita karin harajin da ta ayyana kan hajojin Amurka bisa tanadin dokar hukumar kwastam mai lamba 4 ta shekarar 2025, inda za a dage karin kaso 24 bisa dari na harajin fito a wa’adin kwanaki 90 a zangon farko, amma za a aiwatar da karin kaso 10 bisa dari na harajin da aka ayyana.
- Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha
- Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin
Kazalika, Sin ta kawar da karin harajin fito da aka dora kan hajojin Amurka bisa tanadin doka mai lamba 5 da 6 da hukumar ta kwastam ta sanar a ranakun 9 da 11 ga watan Afirilun da ya shude.
Bisa sanarwar karin haraji da aka fitar cikin watannin da suka gabata, Sin ta kara yawan harajin fito kan kayayyakin Amurka da ke shiga kasar zuwa kaso 84 bida dari da kuma kaso 125 bisa dari, a matsayin martani ga harajin ramuwar gayya da Amurka ta kakabawa kayayyakin Sin dake shiga kasar.
Bugu da kari, sashen lura da haraji na hukumar kwastam ta Sin, ya ce rage haraje-haraje tsakanin kasashen biyu, ya dace da burikan masu sarrafa hajoji da masu sayayya na kasashen 2, zai kuma samar da kyakkyawan yanayin musayar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Amurka da Sin da ma tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp