Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar Sin ta bayyana cewa, a watanni 6 na farkon shekarar 2023, kasar Sin ta yi nasarar dawo da mutane 582 da suka aikata cin hanci da suka gudu zuwa kasashen ketare, tare da kwato kadarori da aka sace ba bisa ka’ida ba na kimanin Yuan biliyan 1.93 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 270.
Wasu bayanan da aka wallafa a shafin yanar gizo na hukumar ladabtarwa ta kwamitin kolin JKS da hukumar sanya ido ta kasa na cewa, daga cikin mutanen da aka dawo da su gida, 25 na cikin jerin sunayen da hukumar ‘yan sandan kasa da kasa wato Interpol, ke nema ruwa a jallo
Kasar Sin na kara fadada nasarorin da ta cimma a fannin yaki da cin hanci da rashawa, ta hanyar kaddamar da ayyuka na musamman, don gano jami’an dake hannu a batakalar cin hanci da rashawa da suka buya a kasashen waje, da kulla hadaka ta hanyar bibiyar wadanda suka tsere, da hana wadanda suka aikata irin barna tserewa da kuma kwato dukiyar da aka sace. (Mai fassara: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp