A kokarin da ake yi na samar da isassun magungunan yaki da cutar COVID-19 a kasar Sin, yanzu haka an fadada adadin yawan magungunan kashe radadin zazzabi, da ciwon jiki nau’in ibuprofen da paracetamol da ake sarrafawa, zuwa sama da kwayoyi miliyan 200 a duk rana, yayin da kuma adadin da ake fitarwa daga kamfanonin sarrafa magungunan a kullum ke kaiwa miliyan 190.
Baya ga haka, adadin maganin zazzabi na yara da ake fitarwa domin bukatar al’umma a yanzu yana kaiwa kwalabe miliyan 1.12 a kullum.
Da yake bayyana alkaluman a taron manema labarai da ya gudana yau Alhamis, mataimakin ministan ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa na kasar Sin Wang Jiangping, ya ce adadin kwayoyin maganin ibuprofen da paracetamol da ake fitarwa daga kamfanonin sarrafa su a yanzu, ya ninka har sau 4, idan an kwatanta da yawan wanda ake fitarwa a farkon watan nan na Disamba, a gabar da kamfanonin da aikin ya shafa a dukkanin sassan kasar Sin ke kara kaimin samar da karin magunguna, da murfin baki da hanci, da alluran rigakafi, da sauran magungunan yaki da cutar ta COVID-19.
A daya hannun kuma, an fadada adadin yawan kayan gwajin cutar ta COVID-19 da ake samarwa, daga kusan miliyan 60 a farkon watan Disamba zuwa kusan miliyan 110 a yanzu.
Wang ya kara da cewa, kasar Sin na kara karfafa tsarin rarraba kayayyakin bukata na kiwon lafiya zuwa dukkanin yankunan kasar. Ya ce ya zuwa jiya Laraba, an riga an rarraba kwayoyin ibuprofen har miliyan 174, da na paracetamol miliyan 60 zuwa muhimman sassan kasar ta Sin. (Saminu Alhassan)