Ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta bayyana cewa, a shekarar 2023, Sin ta ci gaba da fadada hanyoyin sadarwar kasar.
Ma’aikatar ta ce, a shekarar da ta gabata, Sin ta yi nasarar shimfida wayoyin sadarwa na tsawon kusan kilomita miliyan 4.74, wanda ya kawo adadin zuwa kilomita miliyan 64.32 na wayoyin sadarwar kasar.
- Masana’antar Samar Da Kayayyaki Ta Kasar Sin Ta Samu Farfadowa A Shekarar 2023
- An Kammala Gasar Tseren Dawakai Ta Ƙasa-da-ƙasa A Jihar Kano
Bayanai na nuna cewa, kasar Sin tana da kusan tashoshin sadarwa na intanet biliyan 1.14 a karshen shekarar da ta gabata, fiye da miliyan 64.86 kan na shekarar 2022.
A wata takardar bayani da aka fitar a watan da ya gabata, ma’aikatar ta sanar da cewa, kasar Sin na shirin tsawaita fasahar sadarwar wayar salula ta 5G da tsarin wayoyin sadarwa mai saurin Mbps dubu 1 zuwa dukkan gundumomi da garuruwan da ke kan iyakokin kasar nan da karshen shekarar 2025.(Ibrahim)