A yau Talata ne sashen sa ido kan harkokin intanet na kasar Sin ya fitar da wani daftarin dokoki kan yadda ake tafiyar da fasahar tantance hoton fuska, tare da fara neman ra’ayin jama’a kan lamarin.
Hukumar kula da harkokin yanar gizo ta kasar Sin ce ta fitar da takarda dauke da daftarin dokokin. Ta bayyana cewa amfani da fasahar tantance hoton fuska yana bukatar takamaiman dalilai da cikakkiyar larura kuma dole ne a hada da tsauraran matakan kariya. (Mai fassara: Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp