Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ta fitar da jerin manyan matakai na raya yankunan cinikayya maras shinge dake kasar, wadanda za a aiwatar da su tsakanin shekarun 2023 zuwa 2025, a gabar da kasar ke bikin cika shekaru 10 da fara aiwatar da yankunan gwaji na cinikayya maras shinge.
A cewar ma’aikatar, yayin aiwatar da wadannan matakai, yankunan cinikayya maras shinge na kasar za su dora muhimmanci ga cimma nasara a manyan fannoni 164, tsakanin wa’adin shekarar 2023 zuwa 2025, cikin matakan kuwa har da kirkire kirkire a ayyukan manyan hukumomi, da masana’antu mafiya muhimmanci, da gina dandaloli, da kuma aiwatar da manyan ayyuka da shirye shirye.
Tun a shekarar 2013 ne dai kasar Sin ta kafa yankin cinikayya maras shinge na farko a birnin Shanghai, inda daga nan ne kuma yankunan suka rika karuwa zuwa 21. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)