• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Dabarun Warware Rikicin Isra’ila Da Falasdinawa

by CGTN Hausa
2 years ago
Isra'ila

A yau Alhamis ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wata takardar bayanai, mai kunshe da matsaya, da shawarwarin Sin game da dabarun warware rikicin Falasdinawa da Isra’ila.

Takardar ta ce fadan da ya barke a baya bayan nan tsakanin sassan biyu, ya haifar da mummunar asarar rayukan fararen hula, tare da ta’azzara yanayin jin kai. Kaza lika hakan ya haifar da damuwa tsakanin sassan kasa da kasa.

  • Xi Ya Bukaci A Tsagaita Bude Wuta Tare Da Gudanar Da Tattaunawar Zaman Lafiya Kan Rikicin Falasdinu Da Isra’ila
  • BRICS Ta Bi Sahun Sassan Dake Neman Kawo Karshen Rikicin Isra’ila Da Palasdinu

A lokuta mabanbanta, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha fayyace matsayar kasar sa game da rikicin, yana mai jaddada bukatar tsagaita bude wuta nan take, da kawo karshen fadan baki daya, da tabbatar da damar kai kayan agajin jin kai, kana da kare fadadar tashin hankali. Har ila yau, shugaba Xi ya nuna cewa, hanya mafi dacewa ta warware wannan rikici ita ce kafa kasashe biyu masu cin gashin kai, kana kasashen duniya su yi gamayyar tabbatar da zaman lafiya, su yi aiki tare wajen warware batun Falasdinu bisa adalci ba tare da bata lokaci ba.

Bisa kudurorin MDD, kwamitin tsaron majalissar na da alhakin wanzar da zaman lafiya da tsaro tsakanin kasa da kasa, don haka ya zama wajibi kwamitin ya sauke nauyin dake wuyan sa game da batun Falasdinawa.

Game da hakan, Sin ta gabatar da shawarwari 5. Ta daya a aiwatar da cikakken matakin dakatar da bude wuta, da kawo karshen fada baki daya. Ta biyu a tabbatar da kare rayukan fararen hula. Ta uku a tabbatar da samar da agajin jin kai ga masu bukata. Ta hudu a kyautata tsarin shiga tsakani. Kana shawara ta biyar a warware dukkanin matsaloli ta hanyar siyasa. (Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
Daga Birnin Sin

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Next Post
Al’ummun Amurka Sun Yi Kira Ga Kyautata Dangantaka Tsakanin Sin Da Amurka

Al’ummun Amurka Sun Yi Kira Ga Kyautata Dangantaka Tsakanin Sin Da Amurka

LABARAI MASU NASABA

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
APC Da Uba Sani Ba Su Lashe Zaben Gwamnan Kaduna Ba -PDP

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

November 7, 2025
Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

November 7, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu!

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4, Sun Ƙwato Makamai A Filato

Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

November 7, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.