Yau Litinin, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya fitar da takardar bayani kan matakan cimma nasarar sassan tsaron kasa a sabon zamani, da zummar ba da cikakken bayani kan ra’ayi mai kunshe da kirkire-kirkire a bangaren ayyukan tsaro na Sin, da kuma ci gaban da aka samu a wannan bangare ta yadda kasashen duniya za su kara fahimtar ayyuka a sassa daban daban na tsaro da gwamnatin Sin ke gudanarwa.
Takardar ta ce, ayyukan tsaron kasa da kasar Sin ta aiwatar na nacewa hanya ta musamman mai alamar Sin, wadanda ke mai da hankali sosai kan moriyar jama’arta a dukkan fannoni, bisa tushen ka’idar tsaron siyasa da muradun kasa, shi ya sa ayyukan ke tabbatar da samar da ingantaciyyar bunkasuwar kasar mai dacewa da bunkasuwar tattalin arziki da al’ummar kasar, kuma za a iya gyara su bisa halin da tattalin arziki da al’ummun Sin ke ciki, kuma za su ba da tabbaci ga bude kofar kasar ga ketare a sabon mataki, har a kai ga hawa hanyar da ta dace ta tabbatar da doka da shari’a.
Ban da wannan kuma, takardar ta ce, Sin na dora muhimmanci matuka kan hada batun samun bunkasuwa da tabbatar da tsaro tare, ta yadda za a yi kokarin tabbatar da samun ingantacciyar bunkasuwa, da tabbatar da tsaro bisa matsayi mai kyau. A sa’i guda a kai ga hanzarta bude kofa da ba da tabbaci ga sassan tsaron kasar tare. Sin na tsayawa tsayin daka kan kara karfin daidaita harkokin duniya, da nacewa ga ra’ayin tuntubar juna, da yin shawarwari kan daidaita harkokin duniya, da ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban a duniya, kana da yiwa tsarin daidaita harkokin duniya kwaskwarima zuwa hanya mafi dacewa.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp