A yau ne, ofishin kungiyar dake jagorantar aikin raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, wato BRI a takaice, ya fitar da wata muhimmiyar takarda mai taken, hangen nesa, matakan inganta hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”: Makoma mai kyau cikin shekaru 10 masu zuwa.
Wannan takarda ta kunshi kalmomi dubu 133 da sassa guda biyar, wadanda ke bayyana nasarori da aka cimma tare da yin karin haske game da hadin gwiwar gina shawarar a cikin shekaru goma da suka gabata, da baki dayan manufar gina hadin gwiwar shawarar a cikin shekaru goma masu zuwa, da muhimman wurare da hanyoyin ci gaba a cikin shekaru goma masu zuwa, da hanya da matakan ci gaba a cikin shekaru goma masu zuwa, da kuma alkiblar da ake dosa.
Dangane da manufofin raya kasa kuwa, takardar ta ba da shawarar cewa, nan da shekaru goma masu zuwa, dukkan bangarorin za su yi kokarin cimma manufar hadin gwiwa daidai da moriyar juna, da inganta aikin hadin gwiwar aya shawarar zuwa wani sabon mataki na gaba mai inganci. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)