An gudanar da taro na farko na kwamitin raya cinikayya da kiyaye muhalli na hukumar kula da cinikayya ta duniya wato WTO na shekarar 2025 a birnin Geneva dake kasar Switzerland a kwanakin baya, inda tawagar wakilan kasar Sin ta karbi bakuncin taron tattaunawa kan hadin gwiwar fasaha da cinikayya da sana’o’i masu kiyaye muhalli, inda aka gabatar da dabarun Sin na raya sana’o’i da fasaha masu kiyaye muhalli.
A cikin jawabansu, masanan Sin sun yi amfani da ayyukan samar da makamashin da ake iya sake amfani da su, a kasashen Habasha da Sri Lanka da kuma aikin daidaita matsalar wutar lantarki na Afirka da sauransu a matsayin misalan dabarun Sin na hadin gwiwar fasaha. Fasahohin Sin sun kunshi fannnoni uku, na farko shi ne muhimmancin tsara shiri da yin hadin gwiwa, wato kasar Sin ta tsara shirye-shirye da tsarin hadin gwiwa don taimakawa sauran kasashe wajen gudanar da ayyukan yau da kullum na raya fasaha da yanayin aiwatar da shirye-shiryen. Na biyu shi ne aikin da aka gudanar bisa halin da ake ciki, wato kasar Sin ta kiyaye kyautata hadin gwiwar fasaha bisa bukatun wurin don tabbatar da yin amfani da fasahar wajen biyan bukatun raya wurin yadda ya kamata. Na uku shi ne horaswa da gabatar da fasahohi, wato kasar Sin ba ma kawai samar da na’urorin fasaha take yi ba, har da horar da kwararru da ba da ilmi don inganta karfin kwararrun wurin a wannan fanni. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp